Majalisar zartaswar Najeriya ta amince da kasafin kuɗi na 2025 da ya kai naira tiriliyan 47.9.
Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka bayan kammala taron majalisar da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Ya ce kasafin kuɗin ya ƙunshi manyan ayyuka da kuma na musamman da za a gudanar a faɗin ƙasa inda za a miƙa shi gaban majalisar dokoki ta ƙasa domin yin nazari da kuma amincewa da shi.
Ya ce an yi hasashen samun bunƙasar yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kashi 4.6 cikin 100.














































