Home Labaru Karyata Kage: Mnistan Tsaro Ya Ce Ba Shi Ba Ne A Bidiyo...

Karyata Kage: Mnistan Tsaro Ya Ce Ba Shi Ba Ne A Bidiyo Dauke Da Bindiga

28
0

Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan tsaro Janar Bashir Magashi kan kafofin sada zumunta Mohammad Abdulkadri ya fitar ta ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yada wani hoto da cewa ministan ne.

Sanarwar ta ce bincike ya gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon da ake ta yadawa shugaban kwalejin rundunar sojin Najeriya na kimiyya da fasaha da ke Makurɗi wato Nigerian Army College of Environmental Science and Technology (NACEST) ne, wanda muƙaminsa ya ba shi damar riƙe makami idan zai yi tafiya.

Sanarwar ta zayyano wasu abubuwa kamar kalar motar da mutumin ya shiga da takardar dake liƙe a jikin motar da ya dace a ce masu yaɗa bidiyon sun duba kafin su ayyana cewa ministan tsaro ne.

Ta ce ministan na amfani da motar jeep ce ƙirar Land Crusier kuma baƙa kamar sauran takwarorin sa ministoci ba irin wancan motar ba.

Haka kuma, sanarwar ta ce ministan tsaron ba ya buƙatar ya ɗauki bindiga kamar yadda aka gani a bidiyon saboda irin tsattsauran tsaron da ke tattare da muƙamin sa.