Home Labaru Taimaka Wa ‘Yan Bindiga: Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Sojin Bogi A...

Taimaka Wa ‘Yan Bindiga: Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Sojin Bogi A Abuja

30
0

Jami’an hukumar NDLEA da ke hana sha da fataucin miyagun wayoyi a Najeriya sun kama wani sojan bogi da abokin huldar sa yayin da suke safarar kwayoyi da makamai da na’urorin sadarwa ga ƴan bindiga da ke jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama mutanen biyu ne a hanyar Gwagwalada a nan Abuja ranar Juma’a 30 ga Satumban shekarar 2021.

Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya bayyana cewa cikin abubuwan da aka kama su da shi akwai harsasai da aka ɓoye a cikin robar ruwa da wayar sadarwa guda 16 da takardar shaidar aiki da rundunar sojin Najeriya da katunan katin ATM guda 7.

Sannan an kama su da tabar wiwi da ƙwayoyin tramadol da layukan MTN da 9mobile da airtel.

Shugaban hukumar ta NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa ya ba da umarnin a miƙa mutanen da ake zargin ga rundunar sojin Najeriya da wata hukumar leƙen asiri wadda dama ta sa mutanen biyu cikin jerin mutanen da take bincike a kan su.