Home Labaru Kiwon Lafiya Karin Mutum Biyar Sun Mutu A Najeriya Ranar Juma’a

Karin Mutum Biyar Sun Mutu A Najeriya Ranar Juma’a

13
0

Hukumar magance yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC  ta ce Cutar korona ta yi ajalin ƙarin mutum biyar ranar Juma’a a Najeriya.

Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafin ta na intanet, NCDC ta ce an kuma samu ƙarin mutum 176 ɗauke da cutar daga jiha 12, ciki har da nan babban birnin tarayya Abuja.

NCDC tace Jihohin da aka samu karin su ne Abuja (73), Plateau (25), Rivers (20), Kano (18), Lagos (15), Bauchi (9), Osun (8), Ekiti (3), Edo (2), Bayelsa (1), Niger (1), Sokoto (1)

Kawo yanzu jumillar mutum 210,136 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, sai kuma 2,855 da suka mutu, an sallami 198,117 daga wuraren kulawa bayan sun warke.