Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya hori ma’aikata su kara jajircewa, tare da maida himma wajen aiki sakamakon karin albashin da aka yi ma su.
Buhari ya kuma bukaci Kungiyar Kwadago ta Kasa ta nuna nuna dattako wajen yin la’akari da halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki.
Shugaba Buhari ya yi wannan tsokaci ne, yayin da ya ke sa hannu a kan dokar karin mafi kankancin albashi daga naira dubu 18 zuwa naira dubu 30.
Ya ce ya na son ganin a kowane matakin albashi ma’aikaci ya ke, ya kasance ya kara himma wajen kula da aikin sa, sannan ya na so Kungiyar Kwadago ta yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki.
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattawa Ita Enang, ya ce Hukumar Kula da Tsarin Albashi da Ma’ikatar Kwadago ce za su tabbatar ana bin wannan sabon tsari, kuma dokar ta shafi kowane kamfani da ma’aikatu na Nijeriya
You must log in to post a comment.