Gwamnatin tarayya ta ce kimanin mutane miliyan 60 ne ba su da ilimi a Najeriya, ta na mai tabbatar da cewa makarantun yaki da jahilci za su taimaka matuka wajen rage yawan marasa ilimi a fadin kasar nan.
Sakataren ma’aikatar ilimi na tarayya Sonny Echono ya bayyana haka a kwalejin tarayya da ke Otobi, yayin da aka gabatar da cibiyar yaki da jahilci ta yankin arewa ta tsakiya.
Sonny, ya bayyana rashin jin dadin shi a kan yadda yawan marasa ilimi ke karuwa a Nijeriya, tare da bayyana lamarin a matsayin abu ne mai ban tsoro.
Ya ce cibiyoyin yaki da jahilci 104 da za a gina a fadin Nijeriya, za a yi su ne da nufin rage yawan marasa ilimi, kuma gwamnatin tarayya ta fito da tsarin ne saboda yaki da jahilici.
Sakataren ya cigaba da cewa, shirin zai koyar da al’umma ilimin kimiyya da fasaha da kuma lissafi domin sanin hanyoyin magance kalubalen rayuwa.