Home Labaru Sabon Karin Albashi: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Dokar Za Ta Fara...

Sabon Karin Albashi: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Dokar Za Ta Fara Aiki A 18 Ga Watan Afrilu

641
0

Sabon karin mafi karancin albashi na naira dubu 30 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa wa hannu ya fara aiki daga ranar 18 ga watan Afrilu.

Babbar mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin majalisa sanata Ita Enang, ta bayyana haka e ga manema labarai a fadar shugaban kasa a Abuja.

Ta ce rattaba hannu da shugaba Buhari ya yi a kan dokar sabon albashin ta maye gurbin tsohuwar dokar mafi karancin albashi da naira dubu 18.

A cewar sa, dokar zata tilasta wa daukacin ma’aikatan gwamnati da masu zaman kan su biyan naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi.