Home Labaru Karin Albashi: Jam’iyya APC Ta Jinjinawa Buhari Bisa Cika Alkawari Da Ya...

Karin Albashi: Jam’iyya APC Ta Jinjinawa Buhari Bisa Cika Alkawari Da Ya Yi

402
0
Lanre Issa-Onilu, Sakataren Jam’iyar Na Kasa
Lanre Issa-Onilu, Sakataren Jam’iyar Na Kasa

Jam’iyar APC ta jinjinawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa ga sanya hannun kan sabon karancin mafikarancin albashin ma’aikata a Najeriya na naira dubu talatin.

Sakataren jam’iyar na kasa  Lanre Issa-Onilu, ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce hakika wannan doka da shugaba Buhari, ya sanya wa hannu ya cancanci a yaba masa.

Issa-Onilu, ya kuma jinjinawa Majalisun dokoki, da gwamnonin jihohi, da kwamiti na musamman akan tabbatar da sabon tsarin albashin, da kuma kungiyar ‘yan kwadago ta kasa, wandanda ya ce sun taka rawar ganin.

Ya cigaba da cewa ko shakka babu sun cancanci a yaba musu musamman idan akayi la’akari da matsalar tattalin arziki dake fuskantar kasar a wannan lokaci.