Home Labaru Gadara: ‘Yan Bindigar Zamfara Sun Ce Za Sun Rika Kashe Mutane Idan...

Gadara: ‘Yan Bindigar Zamfara Sun Ce Za Sun Rika Kashe Mutane Idan Ba A Janye Jami’an Tsaro Ba

303
0

Wani rahoto da muka samu na cewa ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummar jihar Zamfara sun ce za su cigaba da kashe mutane a jihar, tunda har gwamnatin tarayya ta cigaba da aiko jami’an tsaro domin dakile ayyukan su.

Shugaban ‘yan ta’addan ya bayyana haka a wata hira da suka yi ta sirri da wani sarki a jihar ta Zamfara, wanda jaridar PUNCH ta wallafa.

‘Yan ta’addan, sun nuna rashin jin dadin su akan yadda gwamnatin tarayya ta ke aiko da rundunar tsaro domin daukar mataki a kan su, inada shugaban su ya ce hakan zai kara tunzurasu su cigaba da tada hankalin al’ummar jihar.

Shugaban ‘yan ta’addan wanda ya yi magana da Sarkin, cikin harshen Hausa, ya ce ba za a taba samun zaman lafiya ba tunda har aka kira ‘yan sanda, da sojoji da sauran jami’an tsaro domin su dinga kashe su.Sarkin da suka yi hira ta waya da shugaban ‘yan ta’addan, daya ne daga cikin sarakun a karamar hukumar Zurmi, wacce ke daya daga cikin kananan hukumomin da suke fama da rikici a jihar, sai dai kuma ba a bayyana sunan sa ba.

Leave a Reply