An yankewa wasu ‘yan Najeriya hukuncin kisa a garin Sharjan na kasar hadaddiyar daular larabawa watau UAE bisa samun su da laifin fashi da makamin da sukayi tun a watan Disamban 2016.
‘Yan Najeriyan an same su ne da laifin kai harin fashi da makami kasuwar ‘yan canji a birnin Dubai.
Alkali Majid Al-Muhairi, na kotun sharjah ya yanke hukuncin bayan an tabbatar da laifin da mutanen da suka yi na fashi da makami a kasuwanni canji da na’urar cire kudi wato ATM a kasar Dubai a shekarar 2016.
Mutane 20 aka kama da farko kan zargin laifin kai hari kan jami’an tsaro dake raka motocin kudi zuwa na’uarar ATM a garin Sharjah.
Daga cikin mutane 20, an tabbatar da zargi kan tara kuma an yankewa takwas hukuncin kisa, yayinda na taran ya samu hukuncin watanni shida a gidan yari sannan a koreshi daga kasar.
Rahoton ya nuna cewa sun saci kudi Darhami miliyan 1 da dubu 700 kwatankwacin Naira miliyan 166 da dubu 613 da dari 352, wannan kudin da aka samu a hannun su kenan bayan sun raba sauran tsakanin su sun tura Najeriya.
Jakadan Najeriya a kasar UAE, Mohammed Rimi, ya ce ‘yan Najeriya 446 ne ke kurkukun kasar a yanzu kan laifuka daban-daban da ya hada da safarar muggan kwayoyi da fashi da makami.