Hukumar Kula da jarabawar kammala karatun Sakandare a Nijeriya NECO, ta sanar da korar ma’aikatan ta 70 saboda mallakar takardun kammala karatu na bogi.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar Azeez Sani, ya ce an kori ma’aikatan ne bayan wani kwamitin tantance takardun ma’aikata ya kammala aikin sa da ya hada da gayyatar wadanda ake zargi domin kare kan su.
Ya ce wasu daga cikin ma’aikatan da kan su su ka shaida wa kwamitin cewa takardun su na bogi ne, yayin da kwamitin ya tuntubi wasu makarantun da ma’aikatan su ka ce sun kammala, wadanda su ka musanta takardun shaidar da suka gabatar.
Jami’in ya ce bayan kammala binciken, kwamitin ya mika rahoton sa ga hukumar, wadda ta gabatar wa shugabannin gudanarwar ta domin nazari a kai.
Sani
ya kara da cewa, taron hukumar gudanarwar na 17 ya amince da korar ma’aikatan
70, wadanda ya bayyana su a matsayin matakin farko.