Home Labaru Karar Da Atiku Abubakar Ya Shigar Ba Ta Da Wani Amfani- Buhari

Karar Da Atiku Abubakar Ya Shigar Ba Ta Da Wani Amfani- Buhari

227
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana karar da jam’iyyar PDP, da dan takarar ta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka shigar a matsayin mara amfani a tarihin siyasar Najeriya.

Shugaban kasa ya bukaci kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da ta yi watsi da karar domin ba ta  da wani tasiri.

Shugaban kasa Buhari da jam’iyar APC sun yi korafin cewa baya ga cewar karar da Atiku da PDP suka gabatar ba ta da ma’ana, sannan kuma gaza tabbatar da zarge-zargen kamar yadda yake a cikin kararsu.

Sai dai Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta  PDP sun dage kai da fata, cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Hakan na kunshe ne a jawabin karshe da aka rubuta sannan aka gabatar a gaban kotu, wanda ke sa ran za a aiwatar a ranar 21 ga watan Ogusta, lokacin da kotu za ta saurari bayanan karshe daga jam’iyyu akan karar da Atiku da PDP, suka shigar.