Home Labaru Hukumar EFCC Ta Kwace Fasgo Na Shugabar Ma’aikata Winifred

Hukumar EFCC Ta Kwace Fasgo Na Shugabar Ma’aikata Winifred

282
0
Winifred Oyo-Ita., Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
Winifred Oyo-Ita., Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa EFCC ta kwace mahimman tadardun tafiye-tafiye na shugabar ma’aikatan ta gwamnatin tarayya Winifred Ekanem Oyo-Ita.

Hukumar   EFCC ta kwace mahimman tadardun ne da kuma fasgon ne sakamakon badakalar kudi naira biliyan 3 da take bincike akai wanda kuma ta ke zargi da hannun shugabar ma’aikata a ciki.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin hana Oyo-Ita tserewa daga Najeriya, idan bincike ya yi nisa, sannan duk da cewar shugabar ma’aikatan ta na kwance a asibiti da ke Abuja sakamakon rashin lafiya da take fama da shi, hukumar ta sa wasu jami’anta da za su lura da zirga-zirgan ta.

Wani jami’in hukumar EFCC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da za rar ta sami sauki za su sake gayyatar ta domin ci gaba da amsa tambayoyi, kuma za su gayyaci wasu manyan sakatarori guda uku da wasu daraktoci domin neman karin bayani game da wasu kwangiloli da aka ba wasu kamfanoni dake da alaka da ita. Sai dai ana ta martani, shugabar ma’aikatan ta gwamnatin tarayya Winifred ta ce ba ta da hannu cikin wata badakalar kudi da yawansu ya kai naira billiyan 16, inda ta ce an kirkiri tsarin inshoran ne domin taimaka wa ma’aikacin daya rasu, yayin da ya ke bakin aiki, kuma aikin ta shi ne ta tattara sunayen ma’aikatu da hukumomin da tsarin zai shafa.