Home Labaru Ilimi Wasu Masu Yi Wa Kasa Hidima Ba Su Iya Karanta Haruffan Turanci

Wasu Masu Yi Wa Kasa Hidima Ba Su Iya Karanta Haruffan Turanci

282
0

Hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC ta ce za ta mika sunayen wadanda ke ikirarin kammala karatu, amma ba su iya karatun haruffan turanci ba, ga hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya.

Daraktan hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim,  ne ya bayanna haka a lokacin da yake magana da manema labarai, inda ya ce duk wani dalibin da ya yi karyar yin karatu zai yi shekara biyu a gidan yari.

Birgediya Janar Ibrahim, ya ce akalla matasa masu yi wa kasa hidima milliyan 4 da dubu dari 6 ne aka yaye tun a lokacin da aka kafa hukumar a shekarar 1973.

Ya ce sun sanar da jami’o’i cewa su kula kwarai da gaske kafin su turo dalibai da suka kammala karatu yi wa kasa hidima, saboda duk wanda aka shahadar kammala karatun digiri na bogi za a  mika shi ga jami’an tsaro.

Ya ce abin mamaki shi ne, wasu daga cikin daliban da ke ikirarin sun kammala karatun digiri a jami’a, idan aka ba su ABCD ba za su iya karantawa ba.