Home Labarai ‘YAN SANDA SUN KASHE DAN BINDIGA, SUN CETO MUTANE A ADAMAWA

‘YAN SANDA SUN KASHE DAN BINDIGA, SUN CETO MUTANE A ADAMAWA

1
0

‘Yan sanda a Jihar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta,
sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, tare
da kubutar da wasu mutane biyu da aka sace a karamar
hukumar Toungo.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Adamawa SP Suleiman Nguroje ya bayyana haka a Yola, inda ya ce ya na daya daga cikin nasarorin da rundunar ‘yan sandan ta samu na hada kai wajen kawo karshen garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce an kashe wani mai garkuwa da mutane a lokacin da shi da ‘yan kungiyar sa su ka isa wurin karbar kudin fansa Naira miliyan biyu da aka nema daga ‘yan’uwan ​​wadanda su ka sace.

Nguroje ya kara da cewa, an ceto mutane biyu da su ka hada da wani Suleiman Abdullahi da Ruwa Buba mazauna kauyen Mayo Sumsum da ke karamar hukumar Toungo.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Afolabi Babatola, ya bukaci mazauna yankin su rika sanar da ‘yan sanda inda masu aikata laifuffuka su ke, musamman wadanda aka samu da raunukan harsashi.