Home Labaru Kano Ta Tsakiya: Laila Buhari Ce ’Yar Takarar PDP —Kotu

Kano Ta Tsakiya: Laila Buhari Ce ’Yar Takarar PDP —Kotu

30
0

Kotun Daukaka Kara a karkashin jagorancin Mai Shari’a Itan Mbaba a Kano, ta soke takarar Danburam Nuhu da Jam’iyyar PDP ta gabatar na kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.

Kotun ta amince da zaben fidda-gwani da jam’iyyar ta gudanar a karkashin shugabancin Shehu Sagagi, wanda ya fitar da Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar.

Haka kuma, kotun ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa ta soke sunan Damburam Nuhu, tare da maye gurbin shi da Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Kano ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

A anar 26 ga watan Satumba ne, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar saboda rashin hurumin shari’a, bisa hujjar cewa an shigar da karar ne a Kano maimakon Abuja, sabanin tsarin Majalisar Shari’a ta Kasa a kan al’amuran da su ka shafi kararraki kafin zabe.