Home Labaru Cushen Kasafin Kudi: Ministan Jin Kai Ta Aikawa Takwararta Ta Ma’aikatar Kudi...

Cushen Kasafin Kudi: Ministan Jin Kai Ta Aikawa Takwararta Ta Ma’aikatar Kudi Wasika

72
0

Ministar jin kai Sadiya Umar Faruk ta aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wasika inda ta dora alhakin Cushen Naira Biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta.


Ya zuwa yanzu dai wannan lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ma’aikatun gwamnatin biyu.


A makon jiya, ministar jin kai ta je majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarta, inda wani batu ya taso da ya janyo ce-ce-ku-cen.


A yayin kare kasafin Minista Sadiya Farouk ta dora alhakin bayyanar wadannan Biliyoyin Nairorin kan ma’aikatar kudi ta kasa.


Lamarin da ya kai ga Minista Sadiya Farouk ta rubuta wasika kai tsaye ga ministar kudi Zainab Ahmed.


A cikin wasikar Ministar tace ba ta da hannu a wannan kutsen da kudaden suka yi a kasafin kudin ma’aikatar ta, kuma ta dora laifin akan minister kudim.


To sai dai daga bisani ma’aikatar kudi ta fitar da wata sanarwa, inda ta kare minista Zainab Ahmed daga zargin da minista Sadiya Farouk ta yi mata.

Leave a Reply