Home Labaru Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku

Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku

22
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce zai ware Dala biliyan 10 domin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa Nijeriya a shekara ta 2023.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a birnin Ilorin na Jihar Kwara, yayin kaddamar da gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na Arewa ta Tsakiya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen taimaka wa matasan Nijeriya domin kafa kanana da matsakaitan masana’antu.

Ya kuma bada tabbacin cewa, rashin aikin yi da matasa ke fama da shi a Nijeriya ba a Jihar Kwara ko shiyyar Arewa ta Tsakiya kawai ya tsaya ba.

Atiku Abubakar, ya ce za su tabbatar da cewa a cikin shirin ya yi alkawarin ware Dala biliyan 10 domin ganin an samar da ayyukan yi ga matasa a kananan da matsakaitan sana’o’i.