Majalisar dinkin duniya ta ce wani kiyasi ya bayyana cewar jariri miliyan 78 sabbin haihuwa ne ke fuskantar mummunan hadari na mutuwa duk shekara saboda rashin samun Nonon uwa cikin sa’o’in farko bayan haihuwar su.
Karanta Wannan: Ebola: WHO Ta Koka Da Karuwar Rasa Rayuka A Congo
Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta wallafa tare da hadin gwiwar asusun kulawa da bayar da taimakon gaugawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya ya ce iyaye mata a cikin kasashe 76 dake da matsakaici da kuma karamin karfi, ne cikin jariri biyar ke samun nonon uwa da zarar an haiho su a duniya.
Rahoton ya nuna cewar
jariran da aka ba Nonon-Uwa, bayan dan lokaci kadan da haihuwar shi, sun fi
samun damar rayuwa ba tare da wata matsala ba.