Wani rahoto da kungiyar kula da tsare-tsaren shugabanci PLSI ta fitar, ya bayyana jihohin Kano da Borno da Benue a matsayin jihohi mafi karancin maki wajen bayyana rahoton yadda su ke kashe kudaden gwamnati.
Rahoton mai taken binciken jihohi a kan yadda su ka tafiyar da dukiyar al’umma a shekara ta 2022, ya nuna matakan nuna gaskiya da gwamnati ke bi wajen tafiyar da dukiyar al’umma a hukumance a duk fadin jihohi 36.
Haka kuma, Rahoton wanda ya bayyana jihohin Akwa Ibom da Yobe da Katsina a matsayin wadanda su ka fi samun maki wajen bayyana kudaden da gwamnati ke kashewa, ya nuna cewa jihohi 21 ba su buga cikakken rahoton kudin da su ka kashe ba na shekara ta2021 a yanar gizo, jihohi 19 kuma kwata-kwata ba su buga rahoton kudin ba na shekara ta 2020.
Rahoton, ya ce jihohi 10 ne kawai su ka aiwatar da tanadin dokar kudi na babban ofishin tattara bayanan kudim yayin da jihohi 2 daga cikin 36 su na ci-gaba da kokarin tabbatar da tsarin ga babban ofishin.
You must log in to post a comment.