Home Home Buhari Ya Yaba Wa Anthony Joshua

Buhari Ya Yaba Wa Anthony Joshua

83
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba da nasarar da ɗan wasan damben Birtaniya haifaffen Nijeriya Anthony Joshua ya samu kan abokin karawar sa Jermaine Franklin, a karawar da su ka yi a filin wasan dambe na O2 Arena da ke birnin London.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Tuwita, shugaba Buhari ya ce nasarar da Josua ya samu ta nuna cewa ta hanyar aiki tukuru da sadaukarwa da jajircewa ne ake samun nasara.

Shugaban Buhari, ya yi fatan nasarar ta kasance ɗaya daga cikin nasarorin da ba za a taɓa mantawa da ita ba a tarihin gasar dambe.

Nasarar dai ita ce ta 25 da Joshua ya samu, tun bayan zaman sa fitaccen ɗan wasan dambe a shekara ta 2013.

Leave a Reply