Home Home ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 A Kauyen Taraba

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15 A Kauyen Taraba

94
0

Wasu ‘yan bindiga sama da 60 sun kai hari a kauyen Baka da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba, inda su ka kashe sama da mutane 15.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne daga kogon su da ke saman wani dutse su ka bude wa mutane wuta.

Bayanai sun ce, ‘yan bindigar sun kona gidaje baya ga satar shanu da wawure kayayyaki a shaguna da gidajen mazauna kauyen.

Wani mazaunin garin mai suna Yakubu Garba, ya ce a lokacin da maharan su ka je galibi mazauna kauyen sun tafi sallar Juma’a, daga bisani aka dakatar da sallar kowa ya ranta a na kare domin neman mafaka.

Ya ce adadin wadanda aka kashe ya na iya karuwa, domin wasu da dama sun tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.

Leave a Reply