Home Labaru Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba

Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba

376
0
Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba
Sallar Idi: Gwamnati Ta Bayyana 25 Da 26 Ga Watan Mayu A Matsayin Ranakun Hutu

Gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar coronavarus a Nijeriya.

Sassauta dokar na zuwa ne bayan shawarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba daga kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Nijeriya.

Shugaban Buhari ya amince da shawarar kwamitin na sassauta wasu daga cikin dokokin da aka kafa domin dakile yaduwar annobar a fadin Nijeriya.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce sun ba shugaban kasa shawara a kan matakan da za a dauka a gaba.

Kawo yanzu dai, shugaba Buhari ya amince a bude Masallatai da coci-coci da kasuwanni, bisa sharadin za a bi dokokin da masana harkokin lafiya suka gindaya.

Mustapha ya ce, har yanzu dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi tana nan, sai dai akwai sassauci kan masu jigilar kayan abinci da sauran kayayyakin bukata, sannan an hana duk wani taro da ya haura mutum 20, in banda a wuraren ibada ko kuma wuraren aiki.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa, har yanzu makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe, kana kuma ma’aikatar ilimi ta tarayya za ta samar da tsare-tsaren bude makarantu cikin aminci ba tare da fargaba ba.