Home Labaru Kananan Yara Mata Sun Kai Harin-Kunar-Baki Wake A Jihar Borno

Kananan Yara Mata Sun Kai Harin-Kunar-Baki Wake A Jihar Borno

473
0

Wasu kananan yara mata biyu ‘yan kunar-bakin-wake, sun tada boma-bomai a jihar Borno, inda su ka kashe mutane uku, sannan su ka raunata wasu mutane Takwas kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Shugaban hukumar bada agajin gaugawa ta jihar Borno Bello Danbatta, ya ce ‘yan kunar-bakin-wajen sun kai harin ne a ranar Talatar da ta gabata, da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Mafa.

Ya ce sun shiga garin Mafa ne tare da ayarin wasu Mata da su ka fita karyo itacen girki, a daidai lokacin ne su ka tada boma-boman da ke jikin su.

Boko Haram dai sun kwashe kusan shekaru 10 kenan su na yaki da gwamnati da nufin kafa daular Musulunci a Nijeriya, kuma suna amfani da kananan yara musamman mata wajen kai harin kunar-bakin-wake a masallatai da kasuwanni da gidajen kallo da tashoshin mota.