Home Labaru Kisar ‘Yan Sanda: Buhari Ya Yi Umarnin Bincike Kan Sojoji

Kisar ‘Yan Sanda: Buhari Ya Yi Umarnin Bincike Kan Sojoji

453
0
Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya Damu Na - Buhari
Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya Damu Na - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci shalkwatar tsaron Najeriya ta gudanar da bincike kan kisan wasu jami’an ‘yan sanda 3 da farar hula da rundunar ‘yan sanda ke zargin sojojin bataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba.

Karanta Wannan: IBB Ya Bayyana Nijeriya A Matsayin Kasa Mai Sarkakiya

Babban Hafson Sojin sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, bayan kammala taron majalisar tsaro a karkashin jagorancin shugaban kasa,  ya ce za su gudanar da gagarumin bincike tare da hukunci mai tsanani ga  jami’an da ke  da laifi.

Kamfanin Dillancin labaran Najeriyar ya ce rundunar Sojin da ta ‘yan sanda sun kafa wani kwamitin bincike na hadin gwiwa domin bibiyar lamarin.

A bangare guda mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa,  ya ce bangaren ‘yan sanda ne za su jagoranci kwamitin binciken wanda ya sha alwashin tabbatar da adalci.

Sunayen jami’an ‘yan sandan da sojojin suka kashe sun hada da Saja Usman Dan-Azumi da Saja Dahiru Musa da Sufeta Mark Ediale.

Leave a Reply