Home Labaru An Fara Yi Wa Jami’an Tsaron Nijeriya Binciken Kwakwalwa

An Fara Yi Wa Jami’an Tsaron Nijeriya Binciken Kwakwalwa

374
0

Rundunar tsaro ta farin kaya ta fara binciken kwakwalwa tsakanin jami’an ta da nufin tabbatar da lafiyar su da kuma inganta aikin su.

Ganin yadda ake yawan samun sakin bindiga cikin kuskure tare da kashe rayukan farin kaya da ba su ji ba su gani ba, ya sa kungiyoyin kare hakkin Bil-Adama su ka rika neman a binciki lafiyar kwakwalwar wasu jami’an tsaro da su ke zargin cewa su na wuce gona da iri da kuma harbi ba bisa ka’ida ba.

Rundunar farin kaya ta dauki matakin tabbatar da lafiyar jami’an ne, ta wajen gudanar da wata jarabawa da ta shafi tunani da kwakwalwa.

Daya daga cikin jami’an sashen binciken-kwakwaf da aka tura jihar Adamawa kuma mai magana da yawun rundunar Ali Abari Fika, ya ce an dauki matakin ne, ganin abin da ya faru a wasu jihohi da ya hada da yadda wani jami’in tsaro ya yi barazanar kashe wani ya kuma aikata kisan a Lagos. Ana dai ganin daukar wannan mataki zai taimaka wajen kare martabar aikin soji tare da kara samun kwarewa a aikin da zai zama da muhimmaci wajen cimma buri.