Home Labaru Nasarar Buhari A Kotu: Gwamna Wike Ya Kwaye Wa PDP Baya

Nasarar Buhari A Kotu: Gwamna Wike Ya Kwaye Wa PDP Baya

229
0
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya sabawa tafiyar sa da Jam’iyyar PDP, ta hanyar fitowa fili yana taya Shugaba Buhari murna a kan nasarar da ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

Nyesom Wike, ya ce, yana shelanta sakon goyon bayan na shi ne a sarari saboda ya nuna cewa tun daga birnin zuciyar sa ya fito.

Gwamnan ya ce sakon taya murnar na shi wanda ya yi a fili shi ne mafi inganci fiye da na takwarorin sa na Jam’iyyar PDP da suke ziyartar shugaban kasan a boye.

Wannan abu dai bai yi wa kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP dadi ba, inda suka kalubalance shi cewa in har da gaske yake yi akwai gwamnonin jam’iyyar da ke haka ya fito fili ya fallasa su.

Ana dai ganin wannan wani salo ne da ya sauya a sha’anin siyasar Najeriya wanda masu hasashe ke ganin a tsakanin PDP da APC wa zai fi cin gajiyar shugaban kasa.