Home Labaru Kamfanin WhatsApp Ya Sauya Ka’Idojin Kiyaye Sirri

Kamfanin WhatsApp Ya Sauya Ka’Idojin Kiyaye Sirri

57
0

Shafin sada zumunta na WhatsApp ya sake sauya ƙa’idojin kiyaye sirri bayanda da aka ci shi tara kan rashin kare bayanai a farkon shekarar nan.

Wani Sakamakon bincike ne ya sa wata hukumar kula da kiyaye bayanai ta ƙasar Ireland ta ci kamfanin na Whatsapp tarar fan miliyan 190.

Daga bisani dai WhatsApp ya roƙi a ɗauke masa tarar, amma yana sauya bayanan ƙa’idojin nasa a Turai da Birtaniya domin bin doka.

To sai dai kamfanin yace babu abin da ya sauya daga ainihin yadda yake gudanar da abubuwansa.