Home Labaru Kasuwanci Kamfanin Emirates Ya Sake Soke Zirga-Zirga Zuwa Nijeriya

Kamfanin Emirates Ya Sake Soke Zirga-Zirga Zuwa Nijeriya

114
0

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates mallakar Daular Larabwa, ya sake soke jigilar shiga da fita daga Nijeriya har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa, kamfanin ya ce abokan huldar sa da suka je ko su ka bi ta Nijeriya cikin kwanaki 14 da su ka gabata, ba za a bari su shiga jirgin da zai je Dubai ba, domin a cewar sa, tuni an soke dukkan tikitin da aka saya.

An dai sake dakatar da sufurin ne, kwanaki biyu kacal bayan kamfanin ya sanar da ci-gaba da jigilar bayan shafe makonni da dakatarwa.

Idan dai ba a manta ba, a watan Maris da ya gabata ne kamfanin Emirates ya sanar da dakatar da zirga-zirga zuwa Nijeriya, yayin da ake ci-gaba da sa-in-sa tsakanin gwamnatin tarayya da Daular Larabawa game da gwajin cutar korona.