Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince a ba jihohin Nijeriya 36 tallafin naira biliyan 656 da miliyan 112.
Bayanan tallafin dai sun fito ne, yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa da ya gudana a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo.
A cikin wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban kasa ya fitar, ta ce kowace jiha za ta samu naira biliyan 18 da miliyan 225, wanda za ta biya a cikin shekaru 30 a kan kuɗin ruwa kashi 9 cikin 100.
Fadar shugaban ƙasa, ta ce an ɗauki matakin ne don a tallafa wa jihohi su cimma muradun su na harkokin kuɗi musamman kasafin su na shekara.
Kudaden dai za a raba su ne a matakai shida cikin watanni shida ta hannun Babban Bankin Nijeriya CBN.