Home Labaru Amurka Za Ta Taimaka Wa Nijeriya Shawo Kan Matsalar Tsaro

Amurka Za Ta Taimaka Wa Nijeriya Shawo Kan Matsalar Tsaro

32
0

Kasashen Amurka da Nijeriya, sun sa hannu a kan yarjejeniyar aiki tare a bangarori da dama, inda Amurka ta yi alkawarin taimaka wa Nijeriya wajen shawo kan wasu daga cikin matsalolin da ta ke fuskanta.

Wannan dai wani bangare ne na ziyarar da Sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ke yi a Nijeriya, inda tuni ya gana da shugaba Buhari da wasu manyan jami’an gwamnati.

Yayin ganawar sa da shugaba Buhari, Blinken ya ce Amurka ta maida hankali wajen kulla yarjejeniyar dangantakar diflomasiyya da wasu al’amurra da dama da ake kyautata zaton za su amfani kasashen biyu.

Da ya ke tsokaci a madadin gwamnati, Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya ce tattaunawa tsakanin kasashen biyu ta soma ne tun haduwar shugabannin a wajen taron sauyin yanayi da ya gudana a Glasgow, inda shugaba Joe Biden ya yi alkawarin tallafa wa Nijeriya wajen shawo kan matsalolin da ta ke fuskanta.  

SUFURI: KAMFANIN EMIRATES YA SAKE SOKE ZIRGA-ZIRGA ZUWA NIJ