Shugaban Kamaru Paul Biya ya ba da umarnin sakin wasu fursinoni 333 wadanda aka tsare saboda zarginsu da alaka da masu fafutikar ballewa daga kasar.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ta ce an fasa gurfunar da mutanen a gaban kotun soji.
Wani jami’in gwamnatin Kamaru ya bayyana a wajen wani taron manema labarai cewa suna kokarin sulhu bayan kwashe shekara uku ana rikicin da ya yi ajalin dubban mutane da kuma raba kimanin mutum 500,000 da muhallinsu.
Rikicin ya fara ne a
lokacin da wasu lauyoyi da malamai suka fara yajin aiki dangane da amfani da
Turancin Faransa a kotuna da makarantu a yankin da ke magana da Turancin
Inglishi a yankunan Arewa-maso-Yammaci da kuma Kudu-maso-Yammacin kasar.
You must log in to post a comment.