Home Labaru Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinta-, Osinbajo

Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinta-, Osinbajo

590
0
Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinku-, Osinbajo
Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinku-, Osinbajo

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin Shugaba Buhari za ta kaddamar da karin albashi ga ma’aikatan da albashinsu bai kai matakin da sabon mafi karancin albashin yake ba.

Osinbajo ya fadi wannan maganar ne a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 a yayin da yake karbar bakuncin shuwagabannin kungiyar ‘yan kwadago a fadar shugaban kasa ta Villa.

Shugaban kungiyar TUC Quadri Olaleye shine ya jagoranci tafiyar tare da ministan kwadago Chris Ngige.

Mataimakin shugaban kasan ya jinjinawa kungiyar ‘yan kwadagon inda ya ce: “Zuwanku nan ya tabbatar mana da cewa kun shirya domin yin aiki tare da gwamnatinmu. Ina so ku amince da gwamnatin Buhari, a matsayin wadda kyautatawa ma’aikata ke gaba a cikin kudurorinsa.

“Idan baku manta ba daya daga cikin abinda ya fara yi lokacin da ya amshi gwamnati, shi ne bsi wa gwamnonin jihohi kudin tallafi domin biyan bashi albashin da ma’aikata ke bi.” Haka kuma Osinbajo ya sake jaddada kudurin gwamnatin Buhari na faranta rayuwar ma’aikata inda ya ce akwai kudaden Paris kulob wanda gwamnatin ba tayi kasa a gwiwa ba wurin raba su ga jihohin Najeriya.