Kamfanin na Mark Zuckerberg na shan matsin-lamba daga gwamnatoci da hukumomi a lokuta da dama kan sha’anin sirri da bayanai na masu amfani da Facebook din
Wasu jigogi a gwamnatocin Amurka da Burtaniya da Australia sun nuna damuwa dangane da shirin kamfanin shafin Facebook na hana kutse a cikin sakonnin da ake aikawa ta shafukansa, suna cewa hakan zai iya shafar harkar tsaro.
Cikin wata wasika, babban lauyan gwamnatin Amurka da ministocin cikin gida na Burtaniya da Australia sun bukaci shugaban kamfanin na Facebook, Mark Zuckerberg, da ya dakatar da shirin kange sakonnin da ake turawa a kafofin intanet mallakarsa ciki har da Facebook din, ta yadda sai wanda mai
aika sako da wanda aka tura masa ne kadai za su iya karantawa, ko gani.
Sun jaddada cewa kange sakonnin zai yi cikas ga kamfanonin fasaha wajen gano miyagun ayyuka da ta`addanci.
Sai dai kuma kamfanin
na Facebook ya ce ma`abota dandalin da dangoginsa suna da hakkin sirri dangane
da irin tattaunawar da suke yi ta intanet.
You must log in to post a comment.