Home Labaru Sarkin Musulmi Ya Bukaci Buhari Ya Kawo Karshen Kashe-Kashe A Nijeriya

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Buhari Ya Kawo Karshen Kashe-Kashe A Nijeriya

657
0
Sarkin Musulmi Ya Bukaci Buhari Ya Kawo Karshen Kashe-Kashe A Nijeriya
Sarkin Musulmi Ya Bukaci Buhari Ya Kawo Karshen Kashe-Kashe A Nijeriya

Mai alfarma sarkin musulmi Sa’ad Abubakar na III ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki matakin kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya da makiyan sa.

Mai Alfarmar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da sakataren kungiyar Jama’atu Nasrul Islam Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, mai taken kallubalen tsaro a Nijeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, ‘yan Nijeriya na da ikon bayyana ra’ayoyin su a kan kashe kashen da ake yi a kasar’nan, musamman a yankin Arewa.

Sarkin muslmi ya ce yay i matukar gigita  bisa yawaitar kashe-kashe da salwantar da dukiyoyi sakamakon harin ‘yan bindiga da Boko Haram da kuma masu aikata fyade, inda ya ce matukar gwamnatin ba ta dauki matakan da suka dace za a cigaba da samun afkuwar hare hare a Nijeriya.

Mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga dai, na cigaba da kai hare-hare a jihohin Borno da Katsina da Sokoto da Zamfara da Neja da Adamawa da Kaduna da kuma Taraba, matsalar ta ya kamata ace  ta hana gwamnati barci.

A karshe sa’a abubakar ya yi ga gwamnati ta saurari korafe-korafe mutane da shawarwarin da ake bata domin kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasar nan.