Home Labaru Kama Aiki: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Minsitoci Da Ma’aikatun...

Kama Aiki: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Minsitoci Da Ma’aikatun Su

493
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala rantsar da sabbin ministocin da za su yi aiki a matsayin ‘yan majalisar zartarwar sa.

Wadanda aka rantsar sun kunshi Uchechukwu Ogah (Abia)Ministan Ma’aikatar Tama da Karafa, Muhammad Musa Bello (Adamawa) Ministan Abuja, Godswill Akpabio(Akwa Ibom) Ministan Neja Delta, Chris Ngige(Anambra) Ministan Kwadago, Sharon Ikeazor(Anambra) Karamar Ministar Muhalli, Adamu Adamu(Bauchi) Ministan Ilimi, Maryam Katagum(Bauchi) Ministar Masana’antu Kasuwanci da Zuba Jari, Timipre Sylva(Bayelsa) Karamin Ministan Man Fetur, George Akume(Benue) Ministan Ayyuka Na Musamman, Mustapha Baba Shehuri(Borno) Karamin Ministan Noma da Raya Karkara.

Sauran sune Goddy Jedi Agba(Cross River) Karamin Ministan Lantarki, Festus Keyamo(Delta) Karamin Ministan Neja Delta, Ogbonnaya Onu(Ebonyi) Ministan Kimiyya da Fasaha, Osagie Ehanire(Edo) Ministan Lafiya, Clement Anade Agba (Edo) Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Otunba Richard Adeniyi Adebayo(Ekiti), Ministan Masana’antu da Zuba Jari, Geofery Onyeama(Enugu), Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ali Isa Ibrahim Pantami(Gombe) Ministan Sadarwa, Emeka Nwajiuba(Imo)  Karamin Ministan Ilimi, Suleiman Adamu(Jigawa) Ministan Albarkatun Ruwa, Zainab Shamsuna Ahmad (Kaduna) Ministar Kudi, Muhammad Mahmoud(Kaduna) Ministan Muhalli, Sabo Nanono(Kano) Ministan Harkokin Noma.

Har ila yau Bashir Magashi(Kano) aka nada a matsayin Ministan Tsaro, Hadi Sirika(Katsina) Ministan Sufurin Jiragen Sama, Abubakar Malami (Kebbi) Ministan Shari’a, Ramatu Tijani(Kogi) Karamar Ministar Abuja, Lai Mohammed(Kwara) Ministan Yada Labarai da Al’adu, Gbemisola Saraki(Kwara) Karamar Ministar Sufuri,

Sauran sun kunshi Babatunde Raji Fashola(Lagos) Ministan Ayyuka da Gidaje, Adeleke Mamora(Lagos) Karamin Ministan Lafiya, Muhammad  Abdullahi(Nasarawa) Karamin Ministan Kimiyya da Fasaha, Zubairu Dada(Neja) Karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje, Olamilekan Adegbiti(Ogun) Ministan Tama da Karafa, Tayo Alasoadura(Ondo)  Karamin Ministan Kwadago, Rauf Aregbesola(Osun) Ministan Harkokin Cikin Gida, Sunday Dare (Oyo) Ministan Matasa da Wasanni, Pauline Tallen(Plateau) Ministar Harkokin Mata, Rotimi Amaechi(Rivers)  Ministan Sufuri, Muhammad Maigari Din gyadi (Sokoto) Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Saleh Mamman(Taraba) Ministan Lantarki, Abubakar  Aliyu(Yobe) Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje, sai kuma Sadiya Umar Faruk(Zamfara) Ministar Jin-kai da Walwalar ‘Yan kasa.

Daga cikin ma’aikatun dai a kwai sabbin ma’aikatu biyu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro wadan da su ne ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta Muhammad Maigari Dingyadi, da kuma ma’aikatar kula da harkokin jin kai  da walwalar al’umma ta Sadiya Umar Faruk.
�Νu���