Home Labaru Kalubalen Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 17 A Jihar Katsina

Kalubalen Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 17 A Jihar Katsina

459
0

Al’ummar garin Zakka a jihar Katsina sun ce wasu ‘yan bindiga da ba su san ko su waye ba sun kai masu hari inda suka sace mata 17 tareda kwashe shanu da dukiyoyinsu.

Wani mazauni garin na Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana ya ce ƴan bindigar sun shiga garin ne ranar Lahadi inda suka shafe sama da sa’a biyu suna cin Karen su babu babbakka.

Ya ce ƴan bindigar sun shigo garin ne suka fara harbi wanda hakan ya razana mutanen garin wasu suka shiga daji.

Amma ya ce ɓarayin sun mayar da wata yarinya ƴar wata biyar da haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka ɗauka da ya ce suma Allah ya kuɓutar da su.