Home Labaru Nadin Sarauta : Sarakunan Gargajiya Sun Yi Murabus A Shinkafi

Nadin Sarauta : Sarakunan Gargajiya Sun Yi Murabus A Shinkafi

268
0

Ana ci gaba da cece-kuce a Masarautar Shinkafi da ke jihar Zamfara sakamakon nadin sarautar da aka yi wa Femi Fani-Kayode a matsayin daya daga cikin masu bada shawara kuma ‘dan Majalisar Sarki.

Rahotanni sun ce, Sarkin Shinkafi Alhaji Muhammadu Makwashe Isa ya bai wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriyar wannan mukamin sarautar wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen masarautar saboda sukar da Kayode ke yi wa ai’ummar arewacin kasar nan.

Wannan ya sa wasu daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a masarautar ta Shinkafi suka sanar da ajiye mukamansu saboda nuna rashin amincewa da wannan nadi da suka bayyana a matsayin karan-tsaye ga masarautar shinkafi da kuma arewacin Najeriya baki daya.

Daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu kuma suka bayyana shirin zuwa kotu domin kalubalantar nadin da aka yi wa tsohon ministan, har da Sarkin Shanun Shinkafi, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi.