Home Labaru Jami’an SARS Ta Kama ‘Yan Ta’adda Da Makudan Kudi A Jihar Sokoto

Jami’an SARS Ta Kama ‘Yan Ta’adda Da Makudan Kudi A Jihar Sokoto

399
0
DCP Frank Mba, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda Ta Nijeriya
DCP Frank Mba, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda Ta Nijeriya

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta ta SARS a jihar Sokoto, sun samu kudade da yawan su ya kai naira miliyan goma da manyan bindigogi kirar AK47 guda 8, a hannun wasu masu garkuwa da mutane da su ka sace wani attajirin dan kasuwa Alhaji Tukur Zubairu a Sokoto.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a wajen baje-kolin masu laifin a helkwatar ‘yan sandan SARS da ke Abuja, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Nijeriya DCP Frank Mba, ya ce masu laifin sun hada tawagar aikata ta’addanci a lokacin da su ka hadu a gidan yarin Katsina ne.

Ya ce rundunar ta kama jimillar masu laifi 81 a sassan Nijeriya daban-daban, inda aka samu manyan bindigogi kirar AK47 guda 8, da carbin alburusai 344, da na’ura mai kwakwalwa guda 10 da sauran wasu makamai na gida guda 15.

Jami’an, sun kuma samu nasarar kama ‘yan wata kungiyar ‘yan ta’adda mai hatsari da wani mai suna Rufai ke jagoranta.