Uwargidan shugaban kasa, A’isha Buhari ta fice zuwa birnin dubai na hadaddiyar daular larabawa domin duba lafiyar.
Jaridar Aminiya ta ce ko a karshen makon jiya sai da A’ishan Buharin, ta fita zuwa kasar waje saboda ciwon wuya da ya takura mata jim kadan bayan dawowar ta Abuja daga Legas.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ta fara fama da ciwon wuyan ne tun kusan lokacin da ta dawo daga ta’aziyyar tsohon gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, wanda cutar Corona ta yi ajalin sa.
Aminiya ta gano cewa yanzu haka tana can a wani asibitin da ba a bayyana ba, kuma tana murmurewa.
Sai dai da aka tuntubi mai taimaka wa Uwargidan shugaban kasan kan harkokin yada labarai Barista Aliyu Abdullahi, ya ce ya yi tafiya, ba ya ofis tsawon mako biyu, don haka ba zai iya cewa komai kan batun ba.