Home Labaru Kiwon Lafiya Covid-19: Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Buhari Ya Ba Su Tallafi Don Samar...

Covid-19: Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Buhari Ya Ba Su Tallafi Don Samar Da Cibiyoyin Gwaji

823
0

Kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya agaza mata da kayan tallafi domin rabawa ga al’umonin yakin kuma cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus.

Shugaban Kungiyar gwamnonin yanking Arewa. Simon Lalong

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya yi rokon a ranar Litinin din da ta gabata, jim kadan bayan kammala taron kungiyar da ya gudana a yanar gizo, inda ya ce da tallafin ne za su iya yaki da cutar arewacin Nijeryia.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai ba gwamna lalong shawara a kan harkokin yada labarai Makut Macham, ya ce gwamnonin sun tattauna akan batutuwan da suka shafi annobar COVID-19 da tasirin ra a yakin Arewa.

Haka kuma, gwamnonin sun amince da hanyoyin da ya kamata su bi domin shawo kan annobar, wanda yanzu haka ta kama kusan mutane 400 a Nijeriya, yayin da ta yi sanadiyar mutuwarmutane 10.

Kungiyar gwamnonin ta kuma kuduri tsaurara matakan rigakafi ta hanyar kulle iyakokin jahohi da sa ido da yin aiki tare wajen takaita zirga zirga a tsakanin jahohin, tare da yanke shawarar tuntubar gwamnatin tarayya domin samar da cibiyoyin gwaje gwajen cutar a kowacce jihar da ke Arewacin Nijeriya.