Home Labaru Juyin Mulki : Sojojin Da Suka Hamɓarar Da Shugabar Da Ta Goyi...

Juyin Mulki : Sojojin Da Suka Hamɓarar Da Shugabar Da Ta Goyi Bayan Kisan Musulmai Sun Naɗa Ministoci

217
0

Wani gidan talabijin da ke karkashin ikon soji a Myanmar ya sanar da nadin sabbin ministoci domin maye gurbin waɗanda aka kora daga mulki bayan kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a ranar Litinin.

Jam’iyyar Aung San Suu Kyi, NLD da ta yi nasara a zaben watan Nuwamban da ya gabata ta yi kiran a gaggauta sakin shugabar kasar.

An tsare Suu Kyi, ne fiye da kwana guda bayan soji a Myanmar sun yi juyin mulki tare da tsare manyan zababbun ‘yan siyasa.

Tuni sojojin suka sake buɗe birni na biyu mafi girma a ƙasar na Yangon bayan rufe shi da kuma katse sadarwar Internet.

A halin da ake ciki dai sojoji na kan titunan birnin, da kuma babban birnin kasar Naypyidaw, yayin da suke kara shirin ci gaba da kasancewa a kan mulki.