Home Labaru Juyin Mulki: Kungiyar AU Ta Dakatar Da Guinea

Juyin Mulki: Kungiyar AU Ta Dakatar Da Guinea

23
0
African-Union

Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, ta dakatar da kasar Guinea Conakry daga zama mamba a cikin ta bayan kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde.

A wani sakon twitter, kungiyar ta AU ta ce daga yanzu Guinea Conakry ba za ta kasance cikin dukkanin harkokinta ba saboda kifar da gwamnati da dakarun kasar suka yi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai sojoji a Guinea Conakry suka murkushe gwamnatin kasar tare da kama hambararren Shugaba Alpha Conde.

Shi dai tsohon Shugaba Alpha Conde ya fuskanci suka saboda zargin sa da ake yi da mulkin kama karya.

Matakin kungiyar ta AU, ya zo ne kwana guda da ita ma kungiyar raya arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta dakatar da kasar kasancewa a cikin ta.

Kungiyar ta AU dai ta yi kiran sojojin Guinea Conkary da su gaggauta sakin Alpha Conde.