Home Labaru Gumurzu: Real Madrid Za Ta Buga Wasanni Shida A Watan Satumba

Gumurzu: Real Madrid Za Ta Buga Wasanni Shida A Watan Satumba

14
0
FC Madrid

A karshen makon nan za a ci gaba da wasannin gasar kasashen Turai, inda Real Madrid za ta yi karawa shida a cikin watan kuma cikin fafatawar da za ta yi biyu daga ciki a Champions League za ta kara da Inter Milan da kuma FC Sheriff Trispol ta Rasha.

Sauran wasanni hudu kuwa a La Liga za ta yi da ya hada da kungiyoyin Celta Bigo da Balencia da Mallorca da kuma Billareal kamar yadda hukumar kwallon kafa ta kasar Sipaniya ta tsara.

Real Madrid wadda ta yi wasanni uku a kakar bana a La Liga ta je ta doke Real Betis 1-0 ranar Asabar 28 ga watan Agusta, sai dai kafin wannan wasan na Real Betis Real Madrid ta fara buga gasar La Liga ta bana da cin Alabes 4-1 ranar Asabar 14 ga watan Agusta, sannan ta tashi 3-3 a gidan Lebante ranar Lahadi 22 ga watan Agusta.

Real Madrid wadda ta buga wasanni uku a bana a La Liga a waje, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, lokacin dukkan ‘yan wasa sun koma kungiyoyinsu bayan buga wa kasashensu wasannin shiga gasar kofin duniya.