‘Yan bindigan da ake zargin sun tsere ne daga daga yankunan Bakura – Talata Mafara na jihar Zamfara, a ranar Talata, sun kai hari ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto, inda suka sace a ƙalla mutum 20.
A halin yanzu dai rundunar sojojin Nigeria da wasu hukumomin tsaro suna aikin ragargazar ƴan bindiga a dazukan Zamfara. Saboda aikin da sojojin ke yi an datse hanyoyin sadarwa na salula da kuma kasuwannin sayar da dabbobi da dakatar da sayar da fetur a jarka.
Jihohi irin su Sokoto, Katsina da Niger suma sun ɗauki matakai masu kama da irin na Zamfara. Mazauna Ƙaramar hukumar Dange sun shaidawa manema labarai cewa ƴan bindiga na kwararowa yankin nasu a baya-bayan nan.
Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Garba Moyi ya tabbatar da lamarin amma ya ce gwamnatin tana ɗaukan matakan da suka kamata. Ya ce ƴan bindiga daga Zamfara na shigowa Sokoto amma ba garkuwa da mutane suka yi ba kamar yadda ake yaɗawa sai dai hanyar tserewa suke nema.
Mr Moyi ya tabbatar cewa wasu lokutan ƴan bindigan na kai wa mazauna garin hari don tsorata su ko satar abinci a yayin da suke tserewa.
You must log in to post a comment.