Home Labaru June 12: NADECO Ta Bukaci Buhari Ya Bayyana Abiola A Matsayin Shugaban...

June 12: NADECO Ta Bukaci Buhari Ya Bayyana Abiola A Matsayin Shugaban Kasa

673
0

Jiga-jigan Kungiyar Kare Muradin Siyasar Yarbawa Zalla NADECO, sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sunan marigayi MKO Abiola a matsayin shugaban kasa.

NADECO, ta kuma bukaci a kira kasaitaccen taron makomar Nijeriya domin gano bakin zaren yadda kasar nan za ta cigaba.

Wadanda su ka yi kiran kuwa sun hada da tsohon gwamnan soji na Jihar Lagos Ndubuisi Kanu, da Amos Akingba da Ayo Opadokun.

 Da ya ke karanta takardar bayanin su, Opadokun ya ce irin wannan taron zai kunshi shugabannin dukkan bangarorin kabilun Nijeriya ba wai wasu wakilai da gwamnati za ta nada su wakilci jama’a ba.

Ya ce sun yi wannan kira ne, saboda kafin sojoji su fara mulki a kasar nan a shekara ta 1966, gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin yankuna su na da karfi sosai, kuma su na biya wa al’ummomi dukkan bukatun da su ka wajaba.

Sun ce maida komai dungurugun a hannun gwamnatin tarayya da aka yi ya haifar da cikas a wurare da dama.

Leave a Reply