Home Labaru Zaben 2019: Atiku Ya Yi Daidai Da Ya Maka Buhari A Kotu...

Zaben 2019: Atiku Ya Yi Daidai Da Ya Maka Buhari A Kotu – Jonathan

383
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya ce Atiku Abubakar ya yi daidai da ya kalubalanci nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a zaben shekara ta 2019.

Jonathan ya ce rashin adalci ne a rika kwatanta yanayin zaben shekara ta 2015, wanda ya rungumi kaddara da kuma yadda zaben shekara ta 2019 ya gudana.

Ya ce sabubban da su ka haifar da dalilin da ya sa ya rungumi kaddarar faduwa zabe a shekara ta 2015, kwata-kwata sun sha bamban da irin yadda zabe ya gudana a shekara ta 2019.

Jonathan ya ce, zaben shekara ta 2019, ya wanzu a cikin tashe-tashen hankula da kwamacala da satar akwatu, da kekketa kuri’u da barazana ga jami’an zabe da masu jefa kuri’a.

Har ila yau, Jonathan ya yi amfani da wannan dama, inda ya jinjina wa kan sa wajen kokarin da gwamnatin sa ta yi a bangaren inganta tattalin arziki, inda ya ce da gwamnatin sa ta dore, da tattalin arzkin Nijeriya ya bunkasa fiye da yadda ake ciki a yanzu. 

Leave a Reply