Home Labaru Ranar Dimokradiyya: Za Mu Ci Gaba Kamar China Da Indiya – Buhari

Ranar Dimokradiyya: Za Mu Ci Gaba Kamar China Da Indiya – Buhari

398
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce babu abin da zai hana Nijeriya ci-gaba kamar kasashen China da India ko kuma Indonesia.

Ya ce tun da kasashen China da India da Indonesia su ka cigaba, to babu abin da zai hana Nijeriya ci gaba.

Shugaba Buhari, ya ce kasashen China da Indonesia sun cigaba a karkashin tsarin mulkin mulukiyya, yayin da kasar India ta kai gaci a karkashin tsarin demokradiyya, don haka ya ce babu abin da zai hana Nijeriya kai wa ga gaci.

Buhari ya bayyana haka ne, a wajen bikin murnar ranar dimokradiyya, wadda a karon farko ake tunawa da ita a ranar 12 ga watan Yuni.

An dai sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma rage radadin alhinin soke zaben shugaban kasa na shekara ta 1993.

Leave a Reply