Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnonin Arewa Na Neman Buhari Ya Ba Su Tallafin Coronavirus

Gwamnonin Arewa Na Neman Buhari Ya Ba Su Tallafin Coronavirus

1094
0
Gwamnonin Arewa Na Neman Buhari Ya Ba Su Tallafin Coronavirus.
Gwamnonin Arewa Na Neman Buhari Ya Ba Su Tallafin Coronavirus.

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya agaza mata da kayan tallafi domin raba wa al’umonin yankin da kuma gina cibiyoyin gwajin cutar coronavirus. 

Shugaban Kungiyar kuma gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce da tallafin ne gwamnonin za su iya yaki da cutar a Arewacin Nijeryia.

Kakakin Gwamna Lalong, Makut Macham, ya ce taron gwamnonin a yanar gizo ya tattauna batutuwan da suka shafi annobar COVID-19 da tasirinsa a yakin Arewa.

Gwamnonin sun kuma amince da hanyoyin da ya kamata su bi domin shawo kan annobar, wadda yanzu haka ta kama kusan mutum 400 a Nijeriya, yayin da ta yi sanadiyar mutuwar wasu mutum 10.

Kungiyar gwamnonin ta kuma kuduri tsaurara matakan rigakafi ta hanyar kulle iyakokin jahohi da sa ido da kum yin aiki tare wajen takaita zirga-zirga a tsakanin jahohin.

Sun kuma yanke shawarar tuntubar Gwamnatin Tarayya domin samar da cibiyoyin gwajin cutar a kowacce jihar da ke yankin.