Home Labarai Jinkai: Nijar Ta Gargadi Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Da Su Ringa Bin...

Jinkai: Nijar Ta Gargadi Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Da Su Ringa Bin Ka’Aida

107
0

A jamhuriyar Nijar hukumomin mulkin sojan kasar sun yi
kashedi dangane da yadda suka ce kungiyoyi masu zaman kansu
na gida da na ketare masu aiki a Nijar mafi akasarinsu na aiki ba
tare da kiyaye dokokin kasa ba.


Ministan cikin gidan Nijar, Janar Mohamed Boubacar Toumba wanda ya yi kashedin yayin wani taron manema labarai ya kuma bayyana damuwa kan yaduwar kungiyoyi masu zaman kansu barkatai fiye da 3000 a kasar.\


Ya kara da cewa kungiyoyin na aiki ba tare da bayar da haske kan hanyoyin samar da kudaden shigarsu ba da yadda suke
kashe su. Ma’aikatar cikin gidan ta yi barazanar dakatar da kungiyoyin da ba su kiyaye dokokin aikinsu da dokokin kasa da ma sanar da yiwuwar dakatar da su da ma kama mambobinsu.

Leave a Reply